Tehran ta soma gargadi: Zaɓi diflomasiyya… ko kuma ku tashi tsaye tsaf don wani sabon yaki. Iran ta ce tana nan a shirye, kuma ba za ta ja da baya ba.cikakken bayani 👇
A cewar ministan, Iran ba za ta lamunci matsin lamba ko barazana daga kowace ƙasa ba. Ya ce hanyar da ta fi dacewa ita ce a koma kan tsarin yarjejeniyar nukiliya domin rage tashin hankali da tabbatar da zaman lafiya.
Sai dai ya nanata cewa:
— “Idan wasu ƙasashe suka ƙi yin biyayya ga yarjejeniya, to kada su yi mamakin ganin rikici ya sake ɓarkewa.”
Wannan furuci ya kara tayar da hankali a manyan diplomacies na duniya, musamman ganin yadda Iran ke kokarin nuna karfi da cewa ba za ta durƙusa ba idan aka matsa mata lamba.
#DanmasaniRadio #whiteConnectGL #Darussalam #Iran #Tehran #NuclearDeal #Diplomacy #MiddleEastPolitics #BreakingNews