Yan ta’adda sun halaka shahararriyar jarumar TikTok Mariam CissĂ© saboda goyon bayan sojojin Mali — gwamnati ta ce ba za ta ja da baya ba.cikakken labarin👇
Cikakken bayani:
Masu da’awar jihadi da ke da iko a yankin arewacin Mali sun kashe shahararriyar mai TikTok, Mariam CissĂ©, a bainar jama’a a birnin Tonka, wanda ke cikin yankin Tombouctou.
Rahotanni sun nuna cewa an yi wannan aika-aika ne saboda ta bayyana goyon bayanta ga dakarun gwamnati da ke yaĆ™i da ‘yan ta’adda a yankin.
Mariam Cissé, wacce ke da mabiya fiye da 100,000 a TikTok, ta kasance sananniya wajen yada sakonnin ƙarfafa gwiwa da goyon baya ga sojojin Mali.
Kisan nata ya tayar da hankalin jama’a da kuma fushin gwamnatin mulkin soja, wacce ta fitar da sanarwa tana cewa:
Ba za mu taÉ“a ja da baya ba wajen yaĆ™ar ta’addanci, kuma irin wannan aika-aika ba zai taÉ“a razana mu ba.”
Ba za mu taÉ“a ja da baya ba wajen yaĆ™ar ta’addanci, kuma irin wannan aika-aika ba zai taÉ“a razana mu ba.”