Shin dan Adam zai rayu har shekaru 150? Masanan China sun ce suna kan hanyar kirkirar maganin tsufa — amma masana kimiyya sun ce hujja bata isa ba.karin bayani👇
Masanan Kimiyya na China na ƙoƙarin ƙirƙirar maganin tsawaita rayuwar ɗan Adam har zuwa shekaru 150!
#ScienceNews #China #Longevity #AntiAging #Research #Kimiyya #LabarinDuniya #Technology
Wani kamfani mai suna Longev Biosciences daga kasar China ya bayyana cewa yana bincike kan wani sabon magani da zai iya dakile tsufa tare da tsawaita rayuwa fiye da shekaru 100 — har ma zuwa 150, a cewar ikirarin su.
Sai dai masana kimiyya da dama sun nuna shakku, suna cewa har yanzu babu wata hujja mai ƙarfi da ta tabbatar da cewa wannan maganin na iya yin tasiri kai tsaye wajen tsawaita rayuwa.
A cewar rahotanni, ana amfani da inibi (enzyme inhibitors) wajen gudanar da binciken, wanda ake ganin zai iya rage lalacewar ƙwayoyin jiki da ake dangantawa da tsufa.
#ScienceNews #China #Longevity #AntiAging #Research #Kimiyya #LabarinDuniya #Technology