An mika She Zhijiang, attajirin da ake nema saboda haramtattun caca, daga Thailand zuwa China.karin bayani👇
Rundunar ‘yan sandan Thailand ta tabbatar da cewa an mika She Zhijiang zuwa hukumomin China a ranar Laraba bayan shari’a mai tsawon shekaru uku da ta kai ga kotu ta amince da bukatar mika shi.
She Zhijiang, É—an asalin kasar China, ana zarginsa da gina manyan dandalin caca ta yanar gizo a sassan Asiya da dama, lamarin da ya sa hukumomin kasar suka dade suna nemansa tun kafin a kama shi a Bangkok a 2022.
#SheZhijiang #China #Thailand #Caca #AsiaNews #CrimeUpdate