Xiaomi ta yi gargadi: Farashin wayoyi na iya tashi — saboda hauhawar kudin memory chip!
Kamfanin Xiaomi ya fitar da sanarwar cewa farashin wayoyin salula zai iya ƙaruwa nan gaba, sakamakon tashin da farashin memory chips ya yi a kasuwannin duniya.
Masu masana’antu sun ce hauhawar farashin chip ɗin ya samo asali ne daga:
ƙarancin kayayyakin da ake samu,
karuwar buƙata a duniya,
da kuma tazarar da ake samu a samarwa.
Xiaomi ta bayyana cewa tana ƙoƙarin rage tasirin cost ɗin ga masu saye, amma idan hauhawar ya ci gaba, tilas su tashi farashin wasu sabbin wayoyin. Wannan na nufin cewa masu amfani za su iya fuskantar tsada a sabbin smartphones, musamman waɗanda ke da manyan ajiyar bayanai (RAM/Storage).
Masana sun yi hasashen cewa sauran kamfanonin wayoyi ma ka iya bin wannan hanya idan hauhawar ya ci gaba.
#TechNews #Xiaomi #Smartphones #Economy #MemoryChips #DanmasaniRadio #WhiteConnectGL #Darussalam