An bazama! Jami'an tsaro sun ƙara zafafa bincike don gano ɗaliban da aka sace a Kebbi.


Hukumomin tsaron Najeriya sun bazama a fadin yankin Danko/Wasagu domin karkato bayanai da kuma bibiyar duk wata alamar da za ta kai ga gano dalibai 25 da aka sace daga Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata ta Maga a jihar Kebbi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa jami'an tsaro daga bangarori daban-daban — ciki har da 'yan sanda, sojoji, da Civil Defence — sun shiga daji da yankuna masu nisa don gudanar da bincike.

Hukumar 'yan sanda ta ce za su ci gaba da aikin har sai an kubutar da daliban lafiya, kana suna aiki tare da al’ummomin yankin domin samun sahihan bayanai.

A halin yanzu ana ci gaba da ƙarfafa iyayen daliban da su kwantar da hankalinsu, yayin da gwamnati ke tabbatar da cewa an dukufa wajen ceto yaran ba tare da bata lokaci ba.



#KebbiAbduction #SecurityAlert #NigeriaNews #BringBackOurGirls #SaveKebbiStudents #NaijaUpdates #BreakingNews
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org