Tinubu: Tsare-tsaren gwamnati na nufin murƙushe talauci a tsakanin matasa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa dukkan sabbin tsare-tsaren da gwamnatinsa ke aiwatarwa sun mayar da hankali ne kan yaki da talauci, musamman a tsakanin matasa, domin su samu damar gina kansu da kuma dogaro da kai.
Ya ce gwamnati tana dorawa kan shirye-shiryen horar da matasa, samar da jari, tallafin kasuwanci da habaka fasahohi, domin su zama masu tasiri a kasuwa tare da ƙirƙirar ayyukan yi.
Tinubu ya jaddada cewa an bullo da waɗannan tsare-tsaren ne domin ƙarfafa matasa, rage zaman kashe wando, da kuma tabbatar da cewa kowanne yaro ko yarinya na da kafar da zai taka zuwa nasara.
Shugaban ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta ci gaba da inganta walwalar matasa domin su taka rawar gani wajen gina tattalin arzikin kasa.
#Tinubu #YouthEmpowerment #NigeriaDevelopment #FightPoverty #GovernmentPlans #EconomicGrowth #NaijaUpdates