Sabon shugaban PDP Kabiru Tanimu Turaki ya ce lokaci ya yi da za a mayar da jam’iyya gida ɗaya — haɗin kai ko babu komai.karin bayani 👇


Sabon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Alhaji Kabiru Tanimu Turaki, ya bayyana cewa zai yi duk abin da ya dace domin haɗa kan ’ya’yan jam’iyyar, musamman ganin yadda rikice-rikice da sabani suka dade suna kawo wa jam’iyyar cikas.

A cewarsa, babbar manufarsa ita ce mayar da PDP gida ɗaya, ta yadda za ta zama jam’iyya mai ƙarfi, tsari da mutunta juna, tare da dawo da martabarta a siyasar Najeriya.
Ya ƙara da cewa zaman lafiya da haɗin kai sune ginshiƙin da jam’iyya za ta iya gina nasara a kansu.

Turaki ya kuma yi kira ga tsofaffin shugabanni, manyan jiga-jigai da matasa na jam’iyyar su tashi tsaye wajen goyon bayan sauye-sauyen da za su dawo da ƙarfi da amincewa a cikin jam’iyya.


#DanmasaniRadio #WhiteConnectGL #Darussalam #PDP #NigeriaPolitics #KasaDaKasa #LabaranYau
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org