Shan giya ba kawai yana dagula kai ba — yana lalata hanta a hankali har ya mayar da ita tamkar dutse. cikkaken binciken 👇.
Zaka iya tunanin cewa shan giya lokaci zuwa lokaci ba shi da matsala, amma idan ta yi yawa ta dinga taruwa a jiki, hanta ce ke É—aukar dukkan radadin.
Cututtukan hantar masu alaƙa da giya suna farawa ne lokacin da yawan giya ya tilasta hantarka ta tara kitsen da ya wuce misali cikin ƙwayoyin hanta. Wannan tarin kitse yana haifar da cikewar hanta (inflammation) da raunin ƙwayoyin hanta, wanda a hankali ke rikidewa zuwa tabo (fibrosis).
Idan mutum ya cigaba da shan giya, wannan tabon yana zama mummunan ciwo mai É—orewa (cirrhosis) wanda ba ya dawowa.
Shan giya da yawa a lokaci ɗaya (binge drinking) yana ƙara tsananta wannan kuma lahani ne.Masana sun gano cewa masu shan giya irin haka suna cikin babban haɗarin lalacewar hanta, musamman idan suna da
• gadon cuta (genetic risk), ko
• lalurar jiki kamar ciwon sukari (diabetes).
WaÉ—annan abubuwan ba wai suna aiki ne dabam-dabam ba — suna Æ™arfafa juna, suna sa haÉ—arin ya ninka fiye da yadda ake tsammani.
An kuma gano cewa mata sukan fuskanci mummunar illa duk da shan giya kaÉ—an, saboda jikinsu yana sarrafa giya a wani tsarin dabam wanda ke sa hantarsu ta fi lalacewa da sauri.
Haka kuma, dokokin kiwon lafiya suna taka rawa sosai — takaita sayar da giya, hana tallace-tallacen da ke Æ™arfafa shan giya, da binciken masu fara nuna alamun jaraba na iya rage yawaitar cututtukan hanta.
A takaice: Shan giya ba kawai yana fusata hanta ba —
a hankali yana canza tsarin ginin ta gaba É—aya, ya lalata ta fiye da yadda ake hasashe, musamman idan an haÉ—a shi da matsalolin gado da na jiki.