Hari da tsakar dare: ’Yan bindiga sun sace dalibai 25 a Kebbi.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da cewa an sace dalibai 25 daga Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata ta Gwamnati, Maga, da ke Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu.
Lamarin ya faru ne daren Litinin, kusan ƙarfe 4 na safe, lokacin da ’yan bindiga suka mamaye makarantar.
Sun kashe ma’aikaci ɗaya tare da jikkata wani, kafin daga bisani su yi awon gaba da ɗaliban.
Jami’an tsaro na ci gaba da bincike da ƙoƙarin ceto daliban cikin gaggawa.
#Kebbi #SecurityCrisis #YanBindiga #Maga #DankoWasagu #NigeriaNews #Labarai #SafetyFirst #BringBackOurGirls #ArewaNews