Sabon rikici a Majalisar Dattawa: Akpabio na fuskantar yunkurin tsige shi daga kujerar shugaban majalisa
Lamarin siyasa a Majalisar Dattawa na kara ɗaukar zafi bayan tsohon shugaban marasa rinjaye, Sanata Orji Uzor Kalu, ya zargi wasu ‘yan majalisa da yunkurin tsige shugaban majalisar – Sanata Godswill Akpabio.
Kalu ya bayyana cewa wasu daga cikin Sanatocin suna gudanar da shirin sirri don kifar da Akpabio bisa zargin rashin adalci da fifita wasu a cikin shugabancin majalisa.
Sai dai Akpabio bai ce komai ba tukuna kan wannan zargi, yayin da majalisar ke cikin wani yanayi na siyasar ɓoye-ɓoye da jayayya.
Shin wannan sabon rikici zai haifar da sauyi a jagorancin majalisar dattawa?