Dambarwa a PDP: Kotun tarayya ta dakatar da Babban Taro har sai an warware ƙarar cikin gida
Wannan sabuwar umarni daga kotu na nufin jam’iyyar PDP ba za ta iya ci gaba da shirye-shiryenta na Babban Taron Ƙasa ba har sai an kammala shari’ar da ke gaban kotu.
Masu shigar da ƙarar sun zargi shugabannin jam’iyyar da rashin bin tanade-tanaden kundin tsarin jam’iyyar, wanda a cewar su, zai iya jefa PDP cikin rikicin da zai iya kawo rarrabuwar kai kafin 2027.
Yanzu dai idanu na kan hanyar da jam’iyyar za ta bi domin kaucewa sake fadawa cikin rikicin da ya jima yana addabar ta.