Kano ta yi ɗumi!Dan majalisar tarayya Sagir Koki ya cire hular Kwankwasiyya — ya bar NNPP, me yasa? Ga cikakken bayani 👇
Hon. Engr. Sagir Koki ya cire hular Kwankwasiyya, ya fice daga NNPP!
Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Injiniya Sagir Koki, ya cire hular ja ta Kwankwasiyya a bainar jama’a, alamar ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Koki ya yanke wannan shawarar ne bayan jerin sabani da suka dabaibaye cikin jam’iyyar, musamman kan tsarin tafiyar da harkokin siyasa a jihar Kano.
Kamar yadda ya bayyana, "na yanke shawarar yin abin da na ga ya fi dacewa da mutuncina da muradin mazaɓata", yana mai jaddada cewa zai ci gaba da aiki don ci gaban Kano ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.
Ana rade-radin cewa dan majalisar na iya komawa APC, jam’iyyar da ya fito daga farko kafin ya shiga NNPP a lokacin zaben 2023.