Zazzafar muhawara ta girgiza majalisar wakilai!Kasafin kuɗin 2026 ya haddasa rikici da katse zaman majalisar — ga cikakken bayani 👇
Zazzafar Muhawara ta Tilasta Majalisar Wakilai Tsayawa!
Majalisar Wakilan Najeriya ta katse zaman ta na yau Talata bayan tashin hankali da zazzafar muhawara da ta barke tsakanin ‘yan majalisa yayin tattaunawa kan kasafin kuɗin shekarar 2026.
Rahotanni sun nuna cewa muhawarar ta samo asali ne daga rarrabuwar ra’ayi kan yadda za a ware kuɗaɗen ayyuka da kasafin manyan sassa na gwamnati, inda wasu ‘yan majalisa ke zargin an fifita wasu yankuna da ma’aikatu fiye da wasu.
Shugaban majalisar ya tilasta katse zaman domin kwantar da hankali da dakatar da rikicin kalamai da ya fara ɗaukar zafi tsakanin mambobi.