Jirgin yakin Turkiyya ya fadi a Georgia!Rahotanni sun tabbatar da cewa wani jirgin yakin sojin Turkiyya ya yi hatsari a kasar Georgia yayin atisaye na hadin gwiwa. cikkaken labarin👇
Sojojin Turkiyya 20 sun yi shahada a hatsarin jirgin soji na dakon kaya a Georgia: Ma’aikatar Tsaro
Wani jirgin dakon kaya na Turkiyya ƙirar C-130 wanda ke kan hanyarsa daga Azerbaijan zuwa Turkiyya ya faɗi kusa da kan iyakar Azerbaijan da Georgia.
Ba gano silar hatsarin da adadin waÉ—anda suka rasu ba nan take
17 Mintuna Baya
Ma’aikatar Tsaron Turkiya ta ce sojoji 20 sun yi shahada sakamakon hatsarin jirgin sama na dakon kaya na sojin Turkiyya a Georgia ranar Talata.
"Da misalin Ć™arfe 06:30 na safiya (Ć™arfe 02:30 agogon GMT) tare da haÉ—in gwiwar da hukumomin Georgia, aikin bincike da kuma tawagar masu bincike sun fara bincike kan tarkacen jirgin sojin na dakon kayan da ya faÉ—i a kan iyakar Azerbaijan da Georgia," kamar yadda ma’aikatar ta bayyana ranar Laraba.
Wani jirgin dakon kayan soji na Turkiyya Ć™irar C-130 É—auke da jami’an soji 20 ya yi hatsari kusa da Azerbaijan a kan hanyarsa ta zuwa Turkiyya.
Ma’aikatar ta kuma fitar da sunayen dukkan sojoji 20 da hatsarin ya kashe.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi tattaunawa ta waya ranar Talata da takwaransa na Azerbaijan Ilham Aliyev da kuma takwaransa na Georgia, Firaiminista Irakli Kobakhidze domin nazari kan abin da ya faru a baya bayan nan game da ayyukan bincike da ceto.
Da yake magana a wani taro a babban birnin Ć™asar Ankara, Shugaba Erdogan ya miĆ™a ta’aziyya ga iyalan sojojin da suka yi shahada.
Wasu Ć™asashe da shugabanni daga sassan duniya sun miĆ™a saĆ™onninsu na jaje da ta’aziyya ga Turkiyya bayan hatsarin.
#BreakingNews #Turkiye #Georgia #Sojoji #YakinSoji #DefenceNews #MilitaryUpdate #TurkishAirForce #Security #WorldNews