Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya karɓi baƙuncin Sheikh Ibrahim Isa Makwarari. karin bayani 👇
Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), ya amshi ziyara daga shugaban ɗarikar Qadiriyya a Najeriya, Sheikh Ibrahim Isa Makwarari, tare da tawagarsa jiya talata 11/11/2025 a gidansa dake Abuja. Ziyarar ta kasance cike da girmamawa da tattaunawa kan ci gaban addini da zaman lafiya a ƙasa.