Idan kina bleaching kuma kin fara da Funbact-A, ki sani: ba whitening cream kika fara ba—cutar fata ce kika kunna.ga cikakken binciken nan ƙasa👇
Funbact-A ba cream ne na gyaran fata ko whitening ba. Magani ne da aka haɗa da sinadarai masu ƙarfi uku:
1. Betamethasone – steroid mai lalata tsarin kariyar fata idan aka yi amfani da shi ba daidai ba.
2. Gentamicin – antibiotic da zai iya haddasa juriya ga kwayoyin cuta idan aka yi amfani da shi a hankali.
3. Clotrimazole – antifungal da ba za a iya amfani da shi a kullum ba.
Masu bleaching suna son amfani da Funbact-A saboda yana sa fata ta yi laushi da haske cikin gaggawa, amma wannan hasken ba kyau ba ne—lalacewa ce da aka rufa wa fuska sutura.
Ga matsalolin da ke tattare da amfani da shi wajen bleaching:
1️⃣ Raunin Fata (Skin Thinning)
Steroid ɗin da ke ciki yana cinye kariyar fata, yana sa ta zama taushi kamar takarda. Nan ne matsalolin bleaching ke fara bayyana.
2️⃣ Steroid Acne — Kuraje masu muni
Kwana kaɗan ne za ki fara ganin
manyan kuraje,
ja-ja a fuska,
kumburi,
tabo da ba sa warkewa da wuri.
3️⃣ “Bleaching Veins” – Jijiyoyi su fara bayyana fili
Raunin fata yana sa jijiyoyi su fito kamar igiya a kumatu, hanci da gefen baki.
4️⃣ Tabo irin na ‘Green veins’ da ‘Stretch marks’
Wannan shi ne babban alamar lalacewa: fata ta faɗi, ta tsage, kuma ta lalace sosai.
5️⃣ Fata na daina jure rana (Sunburn & Hyperpigmentation)
Fuska na yin ja, sannan kuma tana yin duhu a wurare saboda lalacewar kariya.
6️⃣ Dogon amfani → Matsalolin hormone
Rashin tsari a amfani da steroid a jiki na iya jawo matsalolin jiki fiye da fata kaɗai.
---
KAMMALAWA:
Funbact-A magani ne, ba bleaching cream ba.
Idan kina/ kana amfani da shi don haske:
ba gyara ake ba—lalacewar fata ake saka a boye.