Ba da yawunmu aka kore Wike daga PDP ba” — Gwamna Fintiri ya bayyana gaskiya. cikakken labarin 👇
Wike bai bar PDP ba, kuma ba mu kore shi ba” — Fintiri ya karyata jita-jita
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ce jam’iyyar PDP ba ta kori Ministan Abuja, Nyesom Wike, daga cikin ’ya’yanta ba, kuma babu wani hukuncin da aka yanke masa da ya kai ga fitarsa daga jam’iyyar.
Fintiri ya bayyana cewa duk maganganun da ake yadawa cewa an kore Wike ko an ɗauke shi a matsayin wanda ya kauce wa jam’iyya “ba da yawun PDP bane”, domin babu wani hukuncin kwamitin ladabtarwa ko na uwar jam’iyya da ya tabbatar da hakan.
Ya kara da cewa Wike har yanzu ɗan PDP ne, kuma jam’iyyar tana da tsarin da take bi kafin ɗaukar matakin hukunci a kan kowane jigo, don haka ba za a yi amfani da tashin hankali ko hayaniyar jama’a wajen yanke hukunci ba.
A cewarsa, rikice-rikicen siyasa da ake gani tsakanin wasu jiga-jigan PDP ba su kai ga korar kowa daga jam’iyya ba, domin “PDP jam’iyyar tsarin dimokaradiyya ce, ba jam’iyyar da ake yanke hukunci da zuciya ba.”