Da Ɗumi-Ɗumi: Ribadu ya dira Amurka kan zargin cin zarafin Kirista —


Mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawaga mai ƙarfi zuwa Amurka domin ganin an warware rikicin zargin cewa ana cin zarafin Kirista a Najeriya.

Wannan bayanin ya fito ne daga majiyoyi a fadar gwamnati, inda aka ce:

Tawagar ta fuskanci wani ɗan majalisar Amurka da ke yada rahoton cewa ana yi wa Kirista kisan kare-dangi a Najeriya.

Sun bayyana masa cewa babu wata manufa ko shirin gwamnati da ke nuna wariyar addini ko kabila.

Sun nemi Amurka ta dogara da sahihan bayanai, ba rahotannin da aka ɓoyewa siyasa ko rashin sani ba.

Sun jaddada cewa gwamnatin Najeriya na gaggauta daukar matakai domin kare rayuka da tabbatar da zaman lafiya — ga kowa, komai addini ko kabila.


An ce ziyarar na da muhimmanci domin dakile mummunar fahimta wadda ka iya jawo matsala tsakanin kasashen biyu.


#DanMasaniRadio #WhiteConnectGL #Darussalam
#NigeriaSecurity #NuhuRibadu #USNigeriaRelations #BreakingNews #NigeriaUpdates #PeaceAndUnity
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org