Kwankwaso ya ce lokaci ya yi da gwamnati ta zurfafa bincike kan tsananta matsalar tsaro a ƙasar.


Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bukaci gwamnatin tarayya ta ɗauki matakai na gaggawa wajen bincike cikin zurfi game da yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na Nijeriya.

Ya ce ya zama wajibi gwamnati ta gano musabbabin da ke hura wutar rikice-rikicen, tare da samar da tsari mai ƙarfi da zai tabbatar da tsaro ga al’umma.
Kwankwaso ya yi gargadin cewa idan ba a tashi tsaye wajen bincike da magance tushen matsalar ba, barazanar na iya haifar da ɗimbin illa ga rayuka, dukiyoyi da ci gaban ƙasa.

#Kwankwaso #SecurityCrisis #NigeriaSecurity #Tsaro #Najeriya #Gwamnati #Bincike #NNPP
Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org