Chelsea yanzu ba ‘yar wasa ba ce.hansi flick
Barça ta gamu da babban ƙalubale! Hansi Flick ya yaba ƙarfin Chelsea, amma ya ce dole ne Blaugrana ta gyara gaban layi da tsarin tsaro idan tana son dawowa da martabarta a Turai.
Hansi Flick ya bayyana cewa Chelsea ta nuna ƙarfin jiki, lamba da tsari wanda ya takura wa Barcelona a kowane sashe na filin. Ya ce wannan wasa ya nuna a fili cewa akwai manyan abubuwa da Barça ke bukatar ta inganta — musamman:
tsaron baya,
dawainiyar tsakiyar fili,
da kare kwallon kai tsaye daga Chelsea.
Flick ya jaddada cewa idan Barcelona ta inganta wadannan fannoni, za ta iya dawo da martabarta cikin manyan kungiyoyin Turai.