Gramma, ta rasu tana kimanin shekaru 141—ƙarni guda da tarihi cikin shiru


Daya daga cikin tsofaffin halittu masu rai a duniya, goggon giwar-kunkurun Galápagos mai suna Gramma, ta rasu bayan fiye da ƙarni guda tana rayuwa cikin natsuwa a San Diego Zoo.

An kiyasta cewa Gramma ta kai kimanin shekaru 141, domin an haifeta ne a asalin mazauninta na tsibirin Galápagos, kafin daga baya ta koma gidan namun daji na Amurka inda ta shafe rayuwarta tana cin abincinta mafi soyuwa: romaine lettuce da ’ya’yan cactus.

Jami’an gidan namun daji sun tabbatar da cewa ta rasu a ranar 20 ga Nuwamba, bayan doguwar rayuwa wadda ta zama wani ɓangare na tarihin namun daji da binciken kiyayewa (conservation).

Rasuwarta ta bar babban gibi a zuciyoyin masu kula da namun daji da masoya halittu a fadin duniya.



#GalapagosTortoise #Gramma #SanDiegoZoo #Wildlife #Conservation #TortoiseLegacy #Duniya #Labarai

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org