Najeriya ƙasa ce mai darajar da yakamata a kare ta - Tsohon Babban hafsan Tsaro

 Tsohon Babban Hafsan Tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce Najeriya tana da darajar karewa, yana kuma kira ga sojoji su ci gaba da jajircewa wajen kare tsaron ƙasa.

Musa ya yi wannan jawabi ne a Abuja yayin bikin bankwana da shi bayan ya yi shekaru 39 yana aiki a rundunar soji.


Ya gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa damar da ya ba shi na hidima, tare da yabawa jami’an tsaro da jama’ar Najeriya saboda goyon bayansu.


Janar Musa ya nuna godiya ga iyalinsa saboda haƙurin da suka yi yayin hidimarsa.


Ya kuma bukaci haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya, yana mai cewa babu hukuma guda da za ta iya samun nasara ita kaɗai.


Musa ya ce duk da cewa ya yi ritaya, zai ci gaba da hidima ga ƙasa ta hanyoyin daban-daban.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org