CBN zata fitar da sabbin takardun kuɗi na N10,000 da N20,000
Wani sabon rahoton tattalin arziki da Quartus Economics ta wallafa ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya fitar da sabbin takardun kuɗi masu ƙima mafi girma kamar N10,000 da N20,000, domin saukaka ɗaukar kuɗin naira da kuma rage tsadar gudanar da harkokin a hannu.
Rahoton mai taken “Is Africa’s Eagle Stuck or Soaring Back to Life?” ya gargadi cewa ci gaba da raguwar ƙimar naira ya sanya takardar N1,000 — wacce ita ce mafi girma a halin yanzu ta zama ba ta da amfani sosai wajen sayayya.
“Domin dawo da sauƙin amfani da kuɗin naira, Najeriya na iya fitar da sabbin takardun N10,000 ko N20,000, ko kuma ta sake ƙirƙirar tsarin ƙimar kuɗinta gaba ɗaya,” in ji rahoton.
Masana sun bayyana cewa, takardar N5,000 da aka yi shirin fitarwa a shekarar 2012 yanzu daidai take da N50,000 a darajar yau, wanda ke nuna raguwar ƙimar gaske ta naira da kashi 94 cikin 100 cikin shekaru ashirin da suka gabata.

 
 
 
