Gwamnatin Tarayya ta fitar da Naira Biliyan 2.3 don biyan bashin Malaman Jami’a

Gwamnatin Tarayya ta fitar da kudi kimanin Naira biliyan 2.3 domin biyan bashin albashin malaman jami’o’in tarayya da sauran ma’aikatan da ake binsu.



Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana haka a jiya Laraba, inda ya ce kudaden da aka saki ta ofishin Akanta Janar na Ƙasa sun nuna jajircewar Shugaba Bola Tinubu wajen biyan basussukan da gwamnati ta gada da kuma inganta walwalar malamai.

Ya ce za a fara karɓar sanarwar biyan kuɗin nan ba da jimawa ba, yayin da gwamnati ke shirin kammala sakin wasu kudade da suka shafi fansho da hakkoki na albashi.

Dakta Alausa ya kara da cewa daga shekarar 2026,  kudin Alawus na EAA zai zama cikakken ɓangare na albashin malaman jami’a domin tabbatar da biyan kuɗaɗe cikin lokaci.

Ya tabbatar da cewa gwamnati tana gudanar da tattaunawa da ƙungiyoyin jami’o’i cikin gaskiya da niyyar tabbatar da zaman lafiya a fannin ilimi.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org