Barayin daji sun sace mataimakin kakakin majalisar dokokin Jihar Kebbi
Rahotanni daga Jihar Kebbi na cewa, mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Samaila Bambu, ya shiga hannun ’yan bindiga da ake zargin ’yan kungiyar Lakurawa ne suka yi garkuwa da shi.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa an sace Bambu ne da yammacin Jumma’a a garinsa na Bagudo, da ke ƙaramar hukumar Bagudu ta jihar.
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Ahmed Idris, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Punch, ya ce yanzu haka yana jiran cikakken rahoton daga daraktan tsaro na jihar kafin a fitar da karin bayani.
