Za a fuskanci hazo tsawon kwana uku a sassan Najeriya - Hukumar Hasashen Yanayi

 Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya, NIMET, ta yi hasashen cewa za a fuskanci yanayin hazo da kura a sassan Najeriya daga yau Litinin zuwa Laraba.

Hukumar ta ce yankunan Arewacin dama na tsakiyar Najeriya ne za su fi fuskantar yanayin na hazo da da kura.

NIMET, ta ce za a samu matsala wajen hangen nesa saboda hazon a tsawon kwanakin ukun.

Daga nan hukumar ta bukaci jama'ar da ke zaune yankunan da hazon zai fi tsanani da su dauki matakan kariya musamman wadanda ke fama da wata lalura data shafi rashin kura ko hazo kamar Asma ko kuma cutukan da suka shafi numfashi.

Kazlaika NIMET, ya shawarci kamfanonin jiragen sama da ke zirga-zirga a Najeriya da su tabbata sun samu cikakken rahoton game da yanayin da za a iya kasancewa da shi a iya kwanakin da aka hasashen fuskantar hazo da kurar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org