An kashe tsofaffi fiye da 100 a Haiti saboda zargin maita
Wata kungiyar kare hakkin dan adam a Haiti ta ce an kashe mutum fiye da 100, galibi tsofaffi bayan wani shugaban 'yan daba a kasar ya zargesu da maita sakamakon rashin lafiyar dansa.
Lamarin ya afku ne a karshen makon da ya wuce.
Kungiyar ta ce lamarin ya faru ne a unguwar Cite Soleil, sannan kuma dukkan mutanen da aka kashen sun haura shekara 60.
An kashe matasa maza ma da dama a yayin da suke kokarin yin zanga zanga don kare iyalansu.
Kafar yada labaran cikin gida a kasar ta ce shugaban ‘yan dabar da aka fi sani da Mikano, y aba wa mutanensu umarnin sace mutanne da ya zarga bayan dan say a fara rashin lafiya, daga nan ne ya bayar da umarnin a kashe su bayan dan ya mutu.
‘Yan dabar sun yi amfani da adduna da bindigogi wajen farwa mtanen inda wasu rahotanni suka ce an kona wasu tsoffaffin ma a raye inda aka binne su a ramuka.
Wasu rahotanni na cewa 'yan daban sun yi amfani da adduna da bindigogi wajewasu har konasu aka yi da wadanda aka binne da ransu a ramuka.
Irin wannan yanayi a Haiti dai ya yi sanadin mutuwar dubban mutane a shekarun baya-bayanan, sai dai matsalar ta ta'azzara a cikin watan da ya gabata, inda 'yan daba masu dauke da muggan makamai ke iko da babban birnin Haitin, Port-au-Prince.