Mai Bautar Kasa Ta Nysc, Yahya Faruq Ya Yi Ɓatan Dabo A jihar Rivers
Jagoran Hukumar Kula da Matasa Masu bautar Kasa (NYSC), Birgediya Janar YD Ahmed, ya yi kira ga daukacin jama’a don hada kai wajen neman matashin, Yahaya Farouk, da ya bace.
Lokacin ziyararsa zuwa garin Ikuru da ke karamar hukumar Andoni a Jihar Rivers, Janar Ahmed ya bukaci matasa da dattawa su taimaka wa hukumomin tsaro wajen gano matashin.
“Dalilin zuwana shi ne neman taimakonku wajen gano matashin da ya zo yin hidima ga kasa daga wata jiha daban,” in ji shi.
Janar Ahmed ya nanata cewa offishin sa zai ci gaba da yin kira don ganin an tabbatar da tsaro da walwala ga duk masu yi wa kasa hidima a kowane lokaci.
Shugaban matasan yankin, Mista Etete Jerb Anthony, da Sakataren Unguwa, Mista Paul Friday, sun tabbatar da cewa ana ci gaba da kokarin nemo matashin Yahaya Farouk, wanda ya bace a wani kamfanin hakar ma’adinai na kasar Sin da ke cikin yankin.