ECOWAS na gab da cimma matsaya na karshe akan amincewa da ficewar kasashen mulkin soja.
Jagororin Kungiyar kasashe (ECOWAS) na shirin cimma matsaya akan kasashen Burkina Faso, Mali, da Jamhuriyar Nijar daga kungiyar a karshen mako mai zuwa, in ba a samu wani sauyi mai kyau ba.
Ana sa ran taron koli na ECOWAS zai fara yau a Abuja, inda za a tattauna batutuwa daban-daban, ciki har da tabbatar da matakin ficewar kasashen uku da ke karkashin mulkin soji.
Sojojin sun karbi mulki ne ta hanyar juyin mulki daban-daban daga shekarar 2020 zuwa bara, lamarin da ya sa ECOWAS ta kakaba musu takunkumi tare da neman a dawo da mulkin farar hula cikin gaggawa.
A wani lokaci, ECOWAS ta yi la’akari da amfani da karfin soji don mayar da shugabanni da aka zaba cikin dimokradiyya, musamman a Jamhuriyar Nijar, kafin ta janye wannan tunani.
Duk da haka, wasu daga cikin takunkumin da aka kakaba wa Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin bara da ya kifar da Mohamed Bazoum an cire su, inda ECOWAS ke amfani da hanyoyin lumana don jan hankalin kasashen su fice.
Sai dai shugabannin sojin sun yi biris da duk wani roko, suna ci gaba da karfafa hadin kansu da juna.
@ATP Hausa