Za a Kara limamai a Masallacin Abuja Kuma za a fara amfani da na'urorin zamani wajen hudubobin Juma'a

 Majalisar Kolin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta sanar da karin sabbin limamai guda biyar ga Masallacin Abuja, inda ta ce akwai yiwuwar karin wasu a nan gaba.

An gabatar da limaman ne ranar Talata a Abuja bayan tantance su da Kwamitin Kudi-Kudi (GPC) tare da amincewa da Kwamitin Fatwa ta Kasa (NFC). Tayi. 

Sabbin limaman guda biyar sun hada da:

Farfesa Ilyasu Usman (Jihar Enugu – baƙo),

Farfesa Luqman Zakariyah (Jihar Osun – mazaunin Abuja),

Dr Abdulkadir Salman (Jihar Kwara – baƙo),

Barrister Haroun Muhammad Eze (Jihar Enugu – mazaunin Abuja), da

Farfesa Khalid Aliyu Abubakar (Jihar Filato – baƙo).

Sakataren Janar na NSCIA, Farfesa Is-haq Oloyede,ne  ya bayyana haks a wajen taron cewa karin sabbin limaman wani yunkuri ne na karfafa Sashen Harkokin Addini na Masallacin Kasa da kuma kara amfani da damar masallacin a matsayin cibiyar ibada, horo, karatu, da bincike a Najeriya.

@ATP Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org