Abin Da Muke Yi Domin Magance Matsalar Tsaro A Najeriya, -Ministan Tsaro Badaru

 A wata tattaunawa da yayi da jaridar (Weekend Trust), mai girma ministan tsaron Najeriya, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, CON, MNI, ya bayyana irin matakan da suke ɗauka domin samar da tsaro a Najeriya ta fuskoki daba-daban ciki har da matakan da suke ɗauka wajen daƙile sabuwar ƙungiyar ƴan’ta’adda ta Lakurawa da ta fara ɓulla a wasu sassa na Arewa maso Yamma, da irin matakan da suke ɗauka wajen samar da alaƙar aiki ta ƙut-da-ƙut a tsakanin rundunonin tsaro, har ma da namijin ƙoƙarin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke yi wajen ganin tsaro ya tabbata a Najeriya.

Da aka yi masa tambaya game da nasarorin da suka cimma a waɗannan watanni sha bakwai da shugaba Tinubu ya shafe a kan mulki, minista Badaru ya bayyana cewa tun daga ranar da aka ba shi muƙamin ministan tsaro a watan Ogas na shekarar 2023, ma'ikatarsa ta samar da tsare-tsare waɗanada suka haɗa da samar da makamai a cikin gida da yin haɗin gwiwa da ƙasashen Duniya.


"Tare da dokar ƙarfafa alaƙa da ma’aikatar samar da makamai ta cikin gida (DICON) da shugaban ƙasa ya sa wa a hannu a ƙarshen shekarar 2023, an tallafawa ma’aikatar ta yadda za ta iya samar da alburusai a cikin gida wanda hakan zai ba mu damar samun sauƙin ƙashe kuɗi da daina dogaro da makaman ƙasashen waje. Daɗi da ƙari, ma’aikatarmu tana aiki kafaɗa da kafaɗa da kamfanoni masu zaman kansu ta fuskar bincike kan harkar tsaro da fasahar zamani a cikin gida". -Mista Badaru.


Ta fuskar farmakar ƴan ta’adda kuwa, minista Badaru ya bayyana cewa sun ƙarfafi sojoji suna samun galaba kan ƙungiyar Boko Haram a Arewa maso Gabas, kuma sun samar da runduna ta musamman ta Fansan Yamma domin fatattakar ƴanbindiga a Arewa maso Yamma da wasu sassa na Arewa ta tsakiya. Baya da haka sun sake ƙarfafa sojojin ruwa ta hanyar samar da sabbin jirage domin magance miyagun laifukan da ke faruwa a gaɓar ruwa da bunƙasa haƙar mai.


Minista ya kuma bayyana matakan da suka ɗauka wajen kyautata walwalar dakaru da kula da lafiyarsu, gami da ƙulla alaƙa da ƙasashen Duniya kan horar da sojoji da kayan aiki gami da amfani da sabbin fasahohi da dabarun aiki na zamani.


Da yake maida jawabi dangane da ƙarancin aiki tare a tsakanin rundunonin tsaro, ministan tsaro Badaru ya bayyana cewa "ma’aikatarmu ta ƙarfafa alaƙar aiki tare a tsakanin rundunonin tsaro da masu ruwa da tsaki ta hanyar ba su horo tare da shirya musu tarukan ƙarawa juna sani da sadarwa a tsakanin gami da ba wa juna bayanai. Baya da haka, tsare-tsare na musamman irin su "Operation Hadin Kai, Operation Whirl Stroke da Operation Safe Haven" suna ba da kyakkyawan sakamako. A ranar bikin ƴancin kai karo na 64, shugaban ƙasa da kansa ya faɗi yadda sojoji suka samu nasarar hallaka ƴan Boko Haram da ƴanbindiga sama da mutum 300 a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da wasu sassan ƙasar". Ya ce.


Ya ƙara da cewa, "mun samu damar dawo da zaman lafiya a ɗaruruwan garuruwa a Arewa, dubban mutane sun samu nasarar komawa garuruwansu. "Daga watan Yuni, 2023 zuwa yau sojojinmu sun samu nasarar hallaka ƴan ta’adda sama da 11,752 tare da kama wasu 11,937 da ake zargi, gami da ceto mutane 7,808 da aka yi garkuwa da su. Daɗi da ƙari, ƴan ta’adda 17,246 da iyalansu sun zubda makamansu sun miƙa wuya". Ya ce.


Minista Badaru ya ƙara da cewa, "daɗi da ƙari mun gano tare da kamo makamai, bindigogi 6,852 da alburusai 145,542 da HH radios guda 127 da motoci 568 da babura 1049 da wayoyin hannu da dama. Sannan a gaɓar ruwa mun samu nasarar daƙile satar ɗanyen mai wanda darajarsa ta kai Naira Biliyan 103, da lalata haramtattun matatun mai da sauransu".


Da aka tambaye shi ko ya yake ji kan wannan muƙami na ministan tsaro da aka ba shi duk da cewa shi ba soja ba ne, minista Badaru ya ce, "hakan ya faru ne duba da ilimin tafikar da mulki da nake da shi, da ƙwarewar da nake da ita ta iya shawo kan matsaloli musamman duba da da kasancewa ta tsohon gwamnan Jihar Jigawa na yi amfani da dabaru sosai wajen shawo kan matsaloli masu tsauri musamman ta fuskar tsaro da tattalin arziƙi wanda hakan ya taimaka wajen magance laifuffuka a Jihar.


Da aka tambaye shi yadda zai yi amfani da ƙwarewarsa wajen magance matsalar tsaro a Arewa maso Yamma kuwa, minista Badaru ya ce "tun bayan zamana minista na maida hankali kan samar da makamai a cikin gida wanda hakan zai ƙarfafa ayyukan sojojinmu tayadda za a samu tsaro a yankin. Sannan kuma gwamnatinmu tana ƙarfafa alaƙa da masu ruwa da tsaki da shugabannin al’umma da kasashe maƙobta domin magance laifuffukan kan iyaka da safarar makamai". Ya ce.


Dangane da sabuwar ƙungiyar ta’addanci ta Lukurawa kuwa, minista Badaru ya maida jawabi da cewa "ina sane da wannan ƙungiya, kuma ma’aikatarmu tana sa ido da lura kan ayyukansu domin daƙile su, za mu yi aiki tare da al’umma da samun bayanan sirri domin kawar da su".


Dangane da ƴan ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) kuwa, minista Badaru ya ce,  "ana samun sauƙinn matsalolinsu ta hanyar tattaunawa da shigo da al’umma, da ɗaukan matakan tsaro na sirri". Ya ce.


In babu tsaro babu wani abu na kasuwanci ko siyasa da zai tafi daidai ko ya gudana wannan ta sa ma’aikataru ta maida hankali wajen samar da rsare-tsare na samar da kykkyawan yanayi na tsaro da zaman lafiya. A matsayina na ministan tsaro na maida hankali kan ƙarfafa tsaron cikin gida da kan iyakoki ta hanyar kyautata walwala da jindaɗin sojoji da inganta ayyuka da fasahar zamani da haɗin gwiwa da ofishin babban mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro da sauran hukumomi.


Dangane da ɗiban sabbin dakaru kuwa, minista Badaru ya ce "ina farin cikin shaida muku cewa ɗaukin aiki yana nan a kowace ma’aikata a lokacin da ya dace. Ina godewa shugaban ƙasa da irin goyon bayan da yake bayarwa wajen ƙara yawan ma’aikata da inganta walwalarsu. Ina jinjinawa sojojinmu da suka sadaukar da kansu domin kare ƙasa. 


Dangane da ziyarar da ya kai Ajaokuta a baya bayan nan kuwa, minista Badaru ya ce "hakan yana da alaƙa ne da ƙoƙarin da nake na ƙarfafa samar da makamai a cikin gida, tun gabanin hakan, ma’aikatar samar da makamai a cikin gida tana wannan aiki da kamfanin na Ajaokuta wajen ƙera makamai da samar da alburusai. Mun fara shirin samar da ƙananan bindigogi. Duk wannan ƙoƙari ne na ganin mun daina dogaro da makaman ƙasashen waje" Ya ce.


Minista Badaru ya kuma bayyana aniyarsu ta amfani da fasahohin na’urorin zamani na AI domin ganin sun taimaka wajen daƙile ayyukan ta’addanci da samar da tsaro a ƙasa, "muna aikin haɗin gwiwa da manyan kamfanonin fasahar zamani na Duniya kan hakan". Ya ce.


Safwan Sani Imam 

Personal Assistant (New Media) to the Honourable Minister of Defence.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org