CBN TA NANATA SAHIHANCIN TSOFAFFIN TAKARDUN N1000, N500, DA N200

 Cikin wata sanarwa da Daraktan Babban Bankin Najeriya (CBN), Hakama Sidi Ali ta fitar, tace CBN ta lura da yadda ake tafka kura-kurai dangane da sahihancin tsofaffin takardun kudi na #1000, 500, da kuma #200 a halin yanzu.

A cewar ta, Dldangane da bayanin da Bankin ya yi a baya da kuma bayar da ƙarin tabbaci, CBN na son sake nanata cewa hukuncin Kotun Koli da aka yanke a ranar 29 ga Nuwamba, 2023, ya ba da izinin cigaba da anfani da duk nau'ikan nau'ikan #1000, 500, da kuma #200 har illa masha allahu.

"Don haka muna shawartar jama’a da su yi watsi da duk wani ikirari na cewa tsofaffin jerin takardun kudin da aka ambata za su daina aiki a doka daga ranar 31 ga Disamba, 2024. Muna kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da karbar duk wata takardar kudin Naira (tsohuwa da na zamani) don hada-hadarsu ta yau da kullum. da kuma rike su da kulawa don tabbatar da tsawon rayuwarsu." A cewar ta.


-Zamani TV

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org