Mai magana da yawun ƴansandan jihar Rivers ta zama lauya
Kakakin Rundunar 'yansandan jihar Rivers ASP Blessing Agabe Karbolo, ta zama cikakkiyar lauya bayan an rantsar da ita a bikin rantsar da sabbin lauyoyi da aka gudanar a Abuja.
Agabe ta bayyana farin cikinta kan wannan nasara, tana mai cewa dukkan godiya ta tabbata ga Allah. Ta ce ta samu wannan nasara ne da amincewar Ubangiji.
'Yar asalin ƙaramar hukumar Tai da ke jihar Rivers ce. Ta shiga aikin 'yansanda a shekarar 2023 bayan kammala karatu a Kwalejin 'yan sandan Najeriya inda ta samu digirin shari'a (LL.B.). Daga bisani ta halarci Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Najeriya da ke Enugu, inda ta samu takardar Barrister-at-Law (B.L.), sannan ta ƙara samun digirin digirgir (LL.M.) daga Jami'ar Jihar Rivers.
A watan Afrilun 2026 ne aka naɗa ta kakakin Rundunar 'yansandan Jihar Rivers. Nasarar da ta samu na zama lauya na ƙara faɗaɗa ƙwarewarta tare da aikinta na jami'ar 'yan sanda.
