Gwamnatin Kano ta farfaɗo da matatar ruwa da ta kwashe shekaru 4 ko ɗigon ruwa ba ta samar ba

 Gwamnatin jihar Kano ta ce ta farfaɗo da matatar ruwa ta Guzu-Guzu, wacce ta ke samar da lita miliyan 7.2 ta ruwa a rana ga yankin kananan hukumomin Kabo da Rimin-Gado.



Kwamishinan Muhalli da Ruwa da Canjin Yanayi, Dr. Dahir M Hashim ne ya baiyana hakan a yau a Kano.


Ya ce aikin farfaɗo da matatar ya haɗa da injin jannareto mai ƙarfin 800KVA, gyaran fayif-fayif hudu da kuma gyaran dakin da ke tunkudo ruwan da kuma ofisoshin ma'aikatan wajen


Hashim ya ce nan da gobe mazauna yankin za su fara ganin ruwa a famfunan su a wani mataki na gwaji yayin da ake ci gaba da aikin don farfaɗo da matatar na dindindin.


Ya ce gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf a shirye ta ke ta farfaɗo da duk karatun ruwa 19 na jihar dan samar da wadataccen ruwan sha ga al'ummar Kano

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org