Tinubu ya umurci karamin ministan tsaro, da ya koma birnin Kebbi nan take —
da ya koma birnin Kebbi nan take — har sai an ceto dukkan ɗaliban da aka sace a jihar.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarni kai tsaye ga karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, da ya yi gaggawar komawa Kebbi don jagorantar dukkan matakan tsaro da ake ɗauka wajen kubutar da ɗaliban da ’yan bindiga suka sace.
An ce gwamnati ba za ta yarda da wani jinkiri ba, kuma an umarci dukkan hukumomin tsaro su hada kai wajen ganin an dawo da yaran lafiya.
#DaDumiDumi #Tinubu #BelloMatawalle #Kebbi #Security #StudentsAbduction #NigeriaNews #BringBackOurStudents #BreakingNews