Sojojin a Najeriya sun gargaɗi: Tsarin kare-kai tsakanin al’ummomi


Sojojin Najeriya sun gargaɗi: Tsarin kare-kai tsakanin al’ummomi, yin haka na ƙara hura wutar rikicin Filato,da sauran bangarorin kasar ba magance shi ba.

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana damuwa kan yadda al’ummomi a wasu yankuna na Jihar Filato ke ɗaukar ɗabi’ar kare kansu daga abokan gaba.
Sojojin sun ce wannan dabarar ba ta kawo zaman lafiya ba — a maimakon haka tana ƙara hura wutar rikici, tana janyo sabbin tashin hankali, da kuma sa rikicin ya bazu fiye da yadda ake tunani.

Sun yi gargadin cewa duk wani mataki na ɗaukar doka a hannu zai iya koma wa al’ummomin da kansu da illa, tare da ƙara dagula yanayin tsaro a jihar. Rundunar ta jaddada cewa gwamnati da jami’an tsaro suna kan aiki don kawo sulhu da kare rayuka, don haka dole ne a guji duk wani mataki da zai ƙara rikici.




#Filato #PlateauCrisis #Tsaro #SojojinNajeriya #NigeriaNews #KareKai #HausaNews #SecurityUpdate
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org