Singapore na ɗaukar mataki na gaba a duniyar blockchain — gwajin tokenised bills da dokokin stablecoin sun kusa fara aiki.karanta kasa,👇
Singapore Ta Fara Gwajin “Tokenised Bills” Kuma Za Ta Kaddamar Da Dokokin Stablecoin – Babban Jami’in Bankin Kasa
Gwamnatin Singapore ta bayyana cewa za ta fara gwajin amfani da takardun bashi (bills) da aka sauya zuwa tsarin dijital ta hanyar “tokenisation,” domin inganta tsarin kasuwanci da biyan kuɗi a cikin tattalin arziki.
A cewar Ravi Menon, babban daraktan Monetary Authority of Singapore (MAS), wannan shirin yana daga cikin yunƙurin kasar na zama cibiyar fasahar kuɗi (FinTech hub) a duniya.
An kuma tabbatar da cewa sabbin dokokin Stablecoin — wato kuɗin dijital da ke da tsayayyen daraja kamar Dala ko Euro — za su fara aiki nan bada jimawa ba, domin kare masu zuba jari da tabbatar da cewa ana amfani da su cikin bin doka.