FG ta soke amfani da harshen uwa a makarantun Najeriya — Ingilishi zai zama harshen koyarwa daga firamare zuwa jami’a. karin bayani 👇

Gwamnatin tarayya ta Najeriya ta soke dokar amfani da harshen uwa a makarantu (National Language Policy – NLP) wadda ta tanadi amfani da harsunan gida a matsayin hanyar koyarwa daga matakin Æ™arami har zuwa firamare. Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana hakan a taron Language in Education International Conference 2025 da aka gudanar a Abuja, inda ya ce Ingilishi yanzu zai zama harshen koyarwa na É—aukacin matakai daga pre-primary zuwa jami’a. 

Ya bayyana cewa bayan nazari kan bayanai daga jihohi da dama, an ga cewa amfani da harshe uwa a matsayin harshen koyarwa ya janyo yadda É—alibai ke samun matsala wajen jarabawar kasa kamar WAEC, NECO da JAMB. “Amfani da harshen uwa ya lalata wasu yankuna na ilimi,” a cewar Alausa. 

Sai dai masana ilimi da na harsuna sun nuna damuwa, suna cewa wannan sauyi na iya kawo cikas ga haÉ“akar harsunan gida, da kuma rarrabuwar ilimi tsakanin birane da karkara. 
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org