Kada ka saurari wanda ya ce ba za ka iya ba!Ka dage, ka gwada, kada ka karaya. Nasara tana jiran wanda bai yarda da kalmomin ƙarya gwiwa ba.
Wani ɗalibi a Jami’ar Columbia da ke ƙasar Amurka ya taɓa yin barci a lokacin da ake gabatar da darasin lissafi. Da ya farka bayan an gama darasin, sai ya ga malamin ya rubuta tambayoyi guda biyu a kan allo.
Sai ya ce a ransa, Wannan tabbas aikin gida ne, sai ya kwafe su a cikin littafinsa domin ya warware su idan ya koma gida.
Ko da ya fara gwadawa, sai ya tarar tambayoyin suna da matuƙar wuya, amma bai karaya ba, sai ya ci gaba da ƙoƙari, yana zuwa ɗakin karatu, yana ta yin bincike a cikin littattafai, sai da ya sha wahala sosai har ya samu da kyar ya iya warware tambaya guda ɗaya.
Da suka dawo karatu a mako na gaba, sai ya lura cewa malamin bai tambayi aikin gida ba. Sai ya ɗaga hannu ya ce:
Malam, me ya sa ba ka tambayi aikin gidan da ka bayar a darasin da ya gabata ba?
Sai malamin ya ce cikin mamaki:
Aikin gida kuma?! Ai ba aiki bane, misalai ne kawai na tambayoyin lissafi wadanda masana kimiyya suka kasa warwarewa tun da dadewa.
Dalibin ya yi mamaki sosai, ya ce:
Amma ni na warware guda ɗaya daga cikinsu, nayi su ne a cikin shafuka huɗu.
Daga nan aka karɓi amsar tambayar tasa a Jami’ar Columbia, kuma aka sanya sunansa a kanta. Har yanzu waɗannan shafuka huɗun suna nan a cikin jami’ar ana nunawa mutane su.
Dalilin da yasa ɗalibin ya samu damar iya warware tambayar abu ne mai sauƙi:
Saboda bai ji lokacin da malamin yake cewa ba wanda zai ya iya warware su ba.
Ya tabbatar wa kansa cewa dole ne a sami mafita, sai ya gwada ba tare da jin tasirin kalmomin ƙarya gwiwa ba, kuma ya ci nasara.
Darasi:
Kada ka saurari wanda suke ce maka ba za ka iya ba. Mafi yawancin matasanmu a yau an karya musu kwarin gwiwa da kuma sanya musu tunanin rashin nasara, musamman saboda wasu mutane da suke ƙoƙarin dasawa zukatansu faɗuwa da gazawa.