Isra’ila ta ce ta buɗe sabon mashigar taimako zuwa Gaza bayan ƙorafe-korafen duniya kan ƙarancin agajin jin-ƙai. Shin hakan zai wadatar da bukatun fararen hula? karin bayani 👇
Bayan tsananin suka daga kungiyoyin agaji da ƙasashen duniya kan yadda ake takaita shigar kayan taimako zuwa Gaza, gwamnatin Isra’ila ta sanar da buɗe sabon babban mashigar agaji a arewacin Gaza Strip.
Wannan matakin ya zo ne yayin da mutane dubban fararen hula ke fama da yunwa, ƙarancin magunguna, da rashin ruwan sha. Kungiyoyin jin-ƙai sun ce buɗe hanya guda ba ta wadatar ba muddin ba a bar kayan taimako su shiga cikin yankunan da ke karkashin yaƙi cikin sauri da tsaro.
Sai dai gwamnatin Isra’ila ta ce ta ɗauki wannan mataki ne don ƙara saurin isar da abinci, ruwa, da magani ga mutanen yankin, tare da tabbatar da cewa kayan ba su faɗa hannun Hamas ba.