Gwamnatin Tinubu ta ce kashe-kashen ‘yan ta’adda sun ragu da kashi 81%!Amma fa…
Wannan na zuwa yayin da gwamnatin Birtaniya ta yi gargadi ga 'yan kasarta da su kaurace wa yin balaguro a wasu sassan Najeriya bayan nuna damuwa kan karuwar hare-haren ta'addanci da satar mutane.
Jihohin da gwamnatin Birtaniya ta yi gargadin sun hada da Borno da Yobe Katsina da Zamfara da Adamawa da Gombe da kuma wasu jihohin na kudanci.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce alkalummanta na shekarar 2025 sun nuna ana samun saukin hare-haren da ake kai wa da satar jama'a.
Gwamnatin ta ƙara da cewa daga shekarar 2024 zuwa yanzu, ta samu nasarar gabatar da ƴanta'adda da ƴanbindiga sama 124 a kotu da aka yanke wa hukunci, sannan ta ce akwai wasu kamar jagororin Ansaru da waɗanda suka kai hari a asibitin Owo a 2022 da na Yelwata da sauransu da suke fuskantar shari'a" ayi caption Wanda zai ja ra'ayin masu karatu don su shiga website