🩺 🌿 Goose Grass — Ciyawar da ke taimakawa wajen dawo da aikin koda, kafin dialysis.👇 lafiya jari

Ciwon Koda: Maganin Gargajiya Mai Amfani da Ciyawar Goose Grass
Idan aka gano mutum yana da ciwon koda, kuma likita ya ambaci yiyuwar fara dialysis (wankin koda), to ka sani akwai wata ciyawa mai matuƙar amfani da ake kira a Turanci Goose Grass (a wasu wurare ana kiranta Couch Grass).

Masu bincike a fannin magungunan gargajiya sun tabbatar da cewa, idan aka yi amfani da wannan ciyawa daidai, tana taimakawa wajen:
✅ Tace jini daga gubobi,
✅ Dawo da aikin koda,
✅ Kara fitar fitsari saboda tana da diuretic effect (yana taimakawa jiki wajen fitar da ruwa mai guba).
Yadda ake amfani da ita:
1️⃣ A samo ciyawar Goose Grass — danya ko busasshiya.
2️⃣ A wanke sosai.
3️⃣ A É—auki kamar tafin hannu É—aya, a dafa da ruwa lita 1 (daidai da kwalban pure water 2).
4️⃣ A tafasa mintuna 20 ko fiye da haka
5️⃣ Bayan ya huce, a tace.

Yadda ake sha:
☀️ Da safe kafin abinci — kofin shayi É—aya.
🌙 Da yamma kafin bacci — kofin shayi É—aya.
A ci gaba da haka na tsawon watanni uku, tare da bin umarnin likita.

Lura:

Kada a bar maganin gargajiya ya maye gurbin kulawar likita.

Duk wanda yake da ciwon koda ko wani ciwo mai tsanani, ya tuntubi likita kafin ya fara amfani da kowanne irin magani.


A ƙasashen China da Indonesia, wannan ciyawa tana daga cikin ganye masu daraja da ake haɗawa da shayi saboda amfaninta ga kodar mutum da tacewar jini.

🕌 Allah Ya ba mu lafiya, Ya tsare mu daga kowanne irin ciwo, Ya sa wannan magani ya zama alheri ga masu amfani da shi da niyyar neman waraka. 🤲Ku yada mana wannan domin Al-umma su amfana
Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org