Gwamna Dikko Radda Ya Nemi Taimakon Belarus Wajen Inganta Tsaro — “Lokaci Yayi da Zamu Dogara da Fasahar Zamani Don Kare Katsina! karin bayani 👇
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda (Ph.D., CON), ya kai muhimmi ziyarar aiki zuwa Cibiyar Tsaron Iyakoki ta Belarus a birnin Minsk, inda ya tattauna da jami’an kasar kan hanyoyin fasahar zamani, musayar bayanan sirri, da horas da jami’an tsaro domin magance matsalolin tsaro a jihar.
Radda ya bayyana cewa iyakar Katsina da Nijar na É—aya daga cikin manyan Æ™alubale wajen tsaro, musamman wajen ta’addanci, safarar makamai, da fataucin mutane, wanda ke bukatar hadin kai tsakanin Æ™asashe da amfani da sabbin dabarun tsaro.
Jami’an Belarus sun yi alkawarin ba da horo, kayan aiki, da tallafin fasaha domin Æ™arfafa tsarin tsaron Katsina. Wannan yunkuri na daga cikin shirin “Building Your Future” na gwamnatin Radda — wanda ke nufin gina makomar matasa da tabbatar da zaman lafiya a jihar.
🗣️ “Katsina na fuskantar kalubalen tsaro da ke bukatar dabaru na zamani da hadin kai na Æ™asa da Æ™asa,” in ji Gwamna Radda.