Masu Ƙwacen Waya Sun Kashe Ma’aikaciyar Lafiya a Zariya.
Wasu da ake zargin masu kwacen waya ne sun kashe wata ma’aikaciyar jinya a Asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya, Jihar Kaduna. Marigayiyar, Hadiza Musa, ita ce mataimakiyar shugabar sashen haihuwa na asibitin.
Mijinta, Hamza Ibrahim Idris, wanda ke aiki a Abuja, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewar an kashe matarsa ne da yammacin Asabar yayin da take dawowa daga aiki.
A cewarsa, A ranar Asabar ta kira shi ta ce za ta je wajen gyaran gashi sannan ta ziyarci wani shagon masu magani a Filin Mallawa, Tudun Wada Zariya, "Na tura mata kuɗi, kuma hakan shi ne maganarmu ta ƙarshe, kimanin ƙarfe 6 na yamma. Bayan haka ban sake samun ta ba.” in ji shu
Ya ce, ya ci gaba da kiran ta har zuwa safiyar Lahadi, yana tunanin cewar cajin wayarta ne ya ƙare. Sai daga baya ne aka gano cewar ta hau babur din haya da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, amma wasu da ake zargin ’yanfashi ne suka tare ta don su kwace wayarta.
“Alamu sun nuna an matse hannayenta da ƙarfi, sannan an bugi kanta har jini ya taru, wanda hakan ne na yi zaton ya jawo mutuwarta,” in ji Hamza Idris.
Bayan an buge ta, barayin sun kwace wayarta sannan suka jefar da ita a gefen titi kusa da filin Idi na Mallawa. Wani mai tausayi ne ya same ta, ya garzaya da ita zuwa wani asibiti, daga bisani aka tura ta Asibitin Koyarwa na ABU Shika, inda aka tabbatar da rasuwarta.
Hamza ya ce marigayiyar ta rasu watanni uku bayan mutuwar ’yar'uwarta, wadda ta bar ’ya’ya uku da ta ɗauka a matsayin nata.
“Ta bar ’ya’yanta uku da kuma waɗanda ta ɗauka bayan rasuwar ’yar uwarta,” in ji shi.
A nasa bangaren, Sakataren Asibitin Gambo Sawaba, Abdulkadir Balele Wali, ya tabbatar da rasuwar Hadiza, yana bayyana ta a matsayin kwararriya mai jajircewa da sadaukarwa, wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen ceton rayukan mata masu juna biyu, “Rasuwarta babban rashi ne ga asibitin gaba ɗaya,” in ji shi.
Sai dai har yanzu rundunar ’yansandan jihar Kaduna ba ta fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, duk da ƙoƙarin da ’yanjarida suka yi na jin ta bakinsu.