Gwamna Bago ya umurci mazauna jihar Neja da su kare kansu

 TSARO A JIHAR NEJA: 

Muryoyi ta ruwaito Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja ya ce ba zai taba shiga tattaunawa da ‘yan bindiga ba, kuma ba zai biya kudin fansa ba ga wadanda aka sace. Ya bayyana haka ne yayin ziyararsa ga al’ummomin Rijau da Magama, inda aka kai hare-hare kwanan nan. 


Gwamnan ya ce, “Idan muka fara biyan fansa, za su dauki hakan a matsayin kasuwanci kuma za su ci gaba da satar mutane.”  Ya kara da cewa ‘yan jihar yanzu suna cikin halin yaƙi, kuma ya zama dole su tashi tsaye domin kare rayukansu da dukiyoyinsu. 


Me zaku ce akai?


✍️ Muryoyi

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org