Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Ce "Me Tinubu ya yi da za a sake zaben shi".
Atiku Abubakar, ya mayar da martani kan furucin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, wanda ya ce ’yan Arewa su hakura da neman kujerar shguaban kasa a 2027, sai 2031 idan Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu.
Jaridar aminiya ta ruwaito George Akume na cewa ’yan Arewa ’yan Jam’iyyar APC mai mulki da ke son neman shugabancin kasa su hakura zuwa 2031, saboda a cewarsa, yanzu lokacin mulkin ’yan yankin Kudu ne, don haka su jira sai Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu.
Ya kuma bukaci Atiku, babban abokin hamayyan Tinubu a zaben 2023 daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP ya hakura ya jira 2021.
Akume ya ci gaba da cewa idan Allah Ya nufi tsohon mataimakin shugaban kasan da zama shugaban kasa zai zama, ko da yana dan shekara 90 ne.
Amma a martanin Atiku, ya bayyana cewa zabin shugaban kasa abu ne da ke hannun ’yan Nijeriya zu zabi wanda suke so.