An Azabtar da Mutane Tare da Tashe Wasu a Gidan Yarin Sadynaya da Aka Samar a Shekarun 1980.
Gidan yarin Saydnaya na Bashar al-Assad da ake yi wa lakabi da mayanka
Tun bayan faduwar gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad na Syria a ranar Lahadin da ta wuce, fararen hula a kasar na ta fatan samun labarin 'yan uwansu da aka kulle a gidan yarin Saydnaya mafi tsaurin tsaro da ya yi kaurin suna.
A shekarun 1980 aka samar da gidan yarin a wani ƙaramin gari da ke da nisan kilomita 30 daga arewacin birnin Damascus.
Gidan yarin Saydnaya, shi ne inda iyalan Assad ke tsare abokan hamayya a lokacin mulkinsu tsawon shekaru.
Gidan yarin da kungiyoyin kare hakkin dan'adam suka yi wa lakabi da mayanka, ana tsare da dubban mutane a ciki inda ake azabtar da su da kuma yanke musu hukunci kowanne iri ne tun shekarar 2011.
@BBC HAUSA