Dokar haraji za ta rushe TETFund, NASENI, NITDA idan aka tabbatar da ita — Zulum
Hukumar Tallafin Ilimi na Manyan Makarantu (TETFund), Hukumar Kasa ta Kimiyya da Injiniyanci (NASENI), da
Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA) za su daina aiki idan har dokokin gyaran haraji guda hudu da Majalisar Dokoki ta Kasa ke tattaunawa sun zama doka.
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ne ya bayyana hakan yayin da yake magana a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels TV, wanda wakilin majiyar mu ya sa ido a ranar Lahadi da daddare.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa dokokin da ake tattaunawa sun hada da:
Dokar Kafa Hukumar Hadin Kai ta Haraji ta Najeriya, 2024 – SB.583
Dokar Kafa Hukumar Haraji ta Najeriya, 2024 – SB.584
Dokar Gudanar da Haraji ta Najeriya, 2024 – SB.585
Dokar Haraji ta Najeriya, 2024 – SB.586.
Zulum, wanda ya ce shi ko wasu gwamnonin Arewacin Najeriya ba su adawa da Shugaba Bola Tinubu kan wadannan dokokin, ya bayyana cewa suna bukatar tattaunawa da karin bayani don kada yankunansu su cutu.
“Wannan tsarin dimokuradiyya ne, muna bukatar karin lokaci. Wasu sun shaida wa Shugaban Kasa cewa gwamnonin suna adawa da shi, amma ba mu ce haka ba. Mun san ikon Shugaban Kasa, ni mutum ne mai biyayya ga tsarin mulki, ina girmama shi. Idan Shugaban Kasa ya yi niyya, zai iya tabbatar da dokokin, amma hakan yana da sakamako ga al’ummar kasa,” in ji Zulum.
“Wani abu da dokar haraji ta tanada shi ne cewa daga shekarar 2029, TETFund za a rushe shi domin kamfanoni za su daina tallafa masa bisa doka… NASENI za a rushe daga 2029… NITDA za a rushe. Wadannan sune damuwarmu,” in ji gwamnan Jihar Borno.
Har ila yau, Zulum ya kara bayyana cewa idan dokokin suka zama doka, jihohi 34 na Tarayyar Najeriya za su yi asara, yayin da Lagos da Rivers za su fi cin gajiyar dokokin.
“Su kawo mana alkaluma da bayanai, su tabbatar mana,” in ji Zulum, yana gargadin cewa za a samu matsaloli ga 'yan Najeriya idan Shugaba Tinubu ya dage wajen tabbatar da dokokin ba tare da la’akari da sakamakon su ba.