Abubuwan Da Yarjejeniyar Najeriya Da Faransa Ta Kunsa

 A makon nan, an ƙulla yarjejeniya tsakanin Najeriya da Faransa don samar da ayyukan hadin gwiwa da zasu inganta harkokin ma’adanai a kasashen biyu.

Ma'adanan sun haɗa da jan karfe (Copper), Lithium, Nickel, da Cobalt. 

A cikin yarjejeniyar da kasashen biyu suka rattaba hannu yayin ziyarar shugaba Bola Ahmed Tinubu ƙasar ta Faransa, sun amince da yin hadin gwiwa kan bincike da horas da daliban ƙasashen biyu domin musayar ilimi da samar da kwarewa.


Babban abin da ke cikin yarjejeniyar shine haɓaka ayyukan hakar ma'adinai masu ɗorewa ta hanyar aiwatar da shirye-shiryen da zasu rage gurɓatar muhalli da ruwa yayin haƙar ma’adinai. 


Ministan ci gaban ma’adanai na Najeriya, Dr Dele Alake ne ya rattaba hannu akan yarjejeniyar a madadin Najeriya, yayin da wakilin ma’aikatar kula da ma’adanai da karafa na Faransa, Benjamin Gallezot, ya sanya hannu a madadin Faransa.


Ana sa ran wannan yarjejeniya za ta bude sabbin damammaki na gyaran ramuka sama da 2,000 da aka yi watsi da su a cikin kasar ta hanyar shirinta na ayyukan gyara muhalli da haƙar ma'adinai.


Wannan yarjejeniyar na daga kokarin gwamnatin Tinubu na inganta bangaren haƙar ma’adinan domin muyi kafaɗa-kafaɗa da takwarorin mu na duniya.


#Focus New Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org